Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 36:4-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Yana ƙulla mugunta lokacin da yake kwance a gadonsa,Halinsa ba shi da kyau,Ba ya ƙin abin da yake mugu.

5. Madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji,Ta kai har sammai,Amincinka ya kai sararin sammai.

6. Adalcinka kafaffe ne,Kamar manyan duwatsu.Hukuntanka kamar teku mai zurfi suke.Ya Ubangiji, kai kake lura da mutane da dabbobi.

7. Ina misalin darajar madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji!Mutane sukan sami mafaka a ƙarƙashin fikafikanka.

8. Sukan yi biki da yalwataccen abincin da yake Haikalinka,Kakan shayar da su daga koginka na alheri.

9. Kai ne mafarin dukan rai,Saboda haskenka ne kuma, muke ganin haske,

10. Ka yi ta ƙaunar waɗanda suka san ka,Ka yi wa adalai alheri.

11. Kada ka bar masu girmankai su fāɗa mini,Kada ka bar mugaye su kore ni.

12. Dubi inda mugaye suka fāɗi!Can suka kwanta, ba su iya tashi.

Karanta cikakken babi Zab 36