Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 35:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka yi hamayya da masu hamayya da ni, ya Ubangiji,Ka yi faɗa da masu faɗa da ni!

2. Ɗauki garkuwa da makamanka, ka zo ka taimake ni.

3. Ka daga mashin yaƙinka sama, da gatarinka,Ka yi gaba da masu fafarata.Ka faɗa mini kai ne Mai Cetona!

4. Ka sa a kori waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni, a kunyatar da su!Ka sa waɗanda suke mini maƙarƙashiya su juya da baya, su ruɗe!

5. Ka sa su zama kamar tattakar da iska take kwashewa,Kamar waɗanda mala'ikan Ubangiji yake korarsu!

6. Ka sa hanyarsu ta duhunta, ta yi santsi,A sa'ad da mala'ikan Ubangiji yake fyaɗe su ƙasa!

7. Suka kafa mini tarko ba dalili,Sun kuma haƙa rami mai zurfi don in faɗa ciki.

8. Amma kafin su farga, hallaka za ta kama su.Tarkunan da suka kafa za su kama su,Su kuma fāɗa cikin ramin da suka haƙa!

9. Sa'an nan zan yi murna saboda Ubangiji,Zan yi murna, gama ya cece ni.

10. Da zuciya ɗaya zan ce wa Ubangiji,“Ba wani kamarka!Kakan kāre marasa ƙarfi daga masu ƙarfi,Talaka da matalauci kuma daga azzalumai!”

11. Mugaye suna ba da muguwar shaida a kaina,Suna kai ƙarata a kan laifofin da ban san kome a kansa ba.

12. Sun sāka mini alheri da mugunta,Cike nake da nadama.

13. Amma sa'ad da suke ciwo, nakan sa tufafin makoki,Na ƙi cin abinci,Na yi addu'a da kaina a sunkuye,

14. Kamar yadda zan yi wa aboki ko ɗan'uwa addu'a.Ina tafe a takure saboda makoki,Kamar wanda yake makoki domin mahaifiyarsa.

15. Sa'ad da nake shan wahala,Murna suke yi duka,Sun kewaye ni, suna ta yi mini dariya,Baƙi sun duke ni, suna ta buguna.

Karanta cikakken babi Zab 35