Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 34:5-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Waɗanda ake zalunta suka dube shi suka yi murna,Ba za su ƙara ɓacin rai ba.

6. Marasa galihu suka yi kira gare shi, ya kuwa amsa.Ya cece su daga dukan wahalarsu.

7. Mala'ikansa yana tsaron waɗanda suke tsoron Ubangiji,Ya cece su daga hatsari.

8. Ku gane da kanku yadda Ubangiji yake da alheri!Mai farin ciki ne mutumin da ya sami kwanciyar rai a wurinsa!

9. Ku yi tsoron Ubangiji ku jama'arsa duka,Masu tsoronsa suna da dukan abin da suke bukata.

10. Har zakoki sukan rasa abinci su ji yunwa,Amma masu biyayya ga Ubangiji,Ba abu mai kyau da sukan rasa.

11. Ku zo, ku abokaina, ku kasa kunne gare ni,Zan koya muku ku ji tsoron Ubangiji.

12. Kuna so ku ji daɗin rai?Kuna son tsawon rai da farin ciki?

13. To, ku yi nisa da mugun baki,Da faɗar ƙarairayi.

Karanta cikakken babi Zab 34