Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 33:15-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Shi ya siffata tunaninsu, yana sane da dukan abin da suke yi.

16. Ba saboda ƙarfin mayaƙa sarki yakan ci nasara ba,Mayaƙi ba yakan yi rinjaye saboda ƙarfinsa ba.

17. Dawakan yaƙi ba su da amfani don cin nasara,Ƙarfin nan nasu ba zai iya ceto ba.

18. Ubangiji yana kiyaye masu tsoronsa,Waɗanda suke dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa.

19. Yakan cece su daga mutuwa,Yakan rayar da su a lokacin yunwa.

20. Ga Ubangiji muke sa zuciya,Shi mai taimakonmu ne, mai kiyaye mu.

21. Saboda da shi muke murna,Muna dogara ga sunansa mai tsarki.

22. Ka sa madawwamiyar ƙaunarka ta kasance tare da mu, ya Ubangiji,Da yake a gare ka muke sa zuciya.

Karanta cikakken babi Zab 33