Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 33:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dukanku adalai ku yi murna,A kan abin da Ubangiji ya yi,Ku yabe shi, ku da kuke masa biyayya!

2. Ku kaɗa garaya, kuna yi wa Ubangiji godiya.Ku raira masa waƙa, da kayan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya.

3. Ku raira masa sabuwar waƙa,Ku kaɗa garaya da gwaninta,Ku kuma raira waƙa da ƙarfi!

4. Kalmomin Ubangiji gaskiya ne,Ayyukansa duka kuwa abin dogara ne.

5. Ubangiji yana ƙaunar abin da yake na adalci da gaskiya,Madawwamiyar ƙaunarsa ta cika duniya.

6. Ubangiji ya halicci duniya da umarninsa,Rana, da wata, da taurari kuma bisa ga maganarsa.

7. Ya tattara tekuna wuri ɗaya.Ya rurrufe zurfafan teku a ɗakunan ajiya.

8. Bari duk duniya ta ji tsoron Ubangiji!Ku ji tsoronsa ku mutanen duniya!

Karanta cikakken babi Zab 33