Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 31:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na zo gare ka, ya Ubangiji, domin ka kiyaye ni.Kada ka bari a yi nasara da ni.Kai Allah mai adalci ne,Ka cece ni, ina roƙonka!

2. Ka ji ni! Ka cece ni yanzu!Ka zama mafakata, don ka kiyaye ni,Ka zama mai kāre ni, don ka cece ni.

3. Kai ne mafakata da kariyata,Ka bi da ni yadda ka alkawarta.

4. Ka kiyaye ni daga tarkon da aka kafa domina,Kai ne inuwata.

5. Ina ba da kaina gare ka domin ka kiyaye ni.Za ka fanshe ni, ya Ubangiji,Kai Allah mai aminci ne.

6. Kana ƙin waɗanda suke yi wa gumaka sujada,Amma ni na dogara gare ka.

7. Zan yi murna da farin ciki,Saboda madawwamiyar ƙaunarka.Ka ga wahalata,Ka kuwa san damuwata.

8. Ba ka bar magabtana su kama ni ba,Ka kiyaye ni.

9. Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji,Gama ina shan wahala,Idanuna sun gaji saboda yawan kuka,Na kuwa tafke ƙwarai!

10. Baƙin ciki ya gajerta kwanakina,Kuka kuma ya rage shekaruna.Na raunana saboda yawan wahalata,Har ƙasusuwana suna zozayewa!

11. Magabtana duka suna mini ba'a,Maƙwabtana sun raina ni,Waɗanda suka san ni kuwa suna jin tsorona,Sa'ad da suka gan ni a kan titi sukan guje mini.

12. Duk an manta da ni kamar matacce,Na zama kamar abin da aka jefar.

13. Na ji magabtana da yawa suna raɗa,Razana ta kewaye ni!Suna ƙulla maƙarƙashiya don su kashe ni.

14. Amma a gare ka na dogara, ya Ubangiji,Kai ne Allahna.

15. Kana lura da ni kullum,Ka cece ni daga magabtana,Daga waɗanda suke tsananta mini.

Karanta cikakken babi Zab 31