Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 30:5-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Fushinsa ba ya daɗewa,Alherinsa kuwa har matuƙa ne.Mai yiwuwa ne yă zama ana kuka da dare,Amma a yi murna da safe.

6. Ina zaune jalisan, na ce wa kaina,“Faufau ba za a taɓa cin nasara a kaina ba.”

7. Kana yi mini alheri, ya Ubangiji,Ka kiyaye ni kamar a kagarar dutse.Amma sa'ad da ka ɓoye mini fuskarka,Sai in cika da tsoro.

8. Ina kira gare ka, ya Ubangiji,Ina roƙon taimakonka.

9. Wane amfani za a samu daga mutuwata?Ina ribar da za a samu daga zuwana kabari?Ko matattu suna iya yabonka?Za su iya shelar madawwamin alherinka?

10. Ka ji ni, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai!Ka taimake ni, ya Ubangiji!

11. Ka mai da baƙin cikinaYa zama rawar farin ciki,Ka tuɓe mini tufafin makoki,Ka sa mini na farin ciki.

12. Don haka ba zan yi shiru ba,Zan raira maka yabo,Ya Ubangiji, kai ne Allahna,Zan gode maka har abada.

Karanta cikakken babi Zab 30