Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 3:5-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Na kwanta na yi barci,Na kuwa tashi lafiya lau,Gama Ubangiji yana kiyaye ni.

6. Ba na jin tsoron dubban abokan gābaWaɗanda suka kewaye ni ta kowane gefe.

7. Ka zo, ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna!Ka yi nasara a kan dukan abokan gābana,Ka hallakar da dukan mugaye.

8. Ceto yana zuwa daga wurin Ubangiji,Bari yă sa wa jama'arsa albarka!

Karanta cikakken babi Zab 3