Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 28:2-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ka ji ni lokacin da na yi kuka gare ka neman taimako,Ina ɗaga hannuwana wajen tsattsarkan Haikalinka.

3. Kada ka kāshe ni tare da mugaye,Tare da masu aikata mugunta,Mutane waɗanda maganarsu kamar ta zumunci ce,Amma zukatansu cike suke da ƙiyayya.

4. Ka hukunta su saboda abin da suka aikata.Ka hukunta su saboda dukan ayyukansu,Ka ba su abin da ya cancance su!

5. Ba su kula da abin da Ubangiji ya yi ba,Ko kuma abin da ya halitta,Don haka zai hukunta su, ya hallaka su har abada.

6. A yabi Ubangiji,Gama ya ji kukana na neman taimako!

7. Ubangiji yakan kiyaye ni, yă tsare ni.Na dogara gare shi.Ya taimake ni, don haka ina murna,Ina raira masa waƙoƙin yabo.

8. Ubangiji yana kiyaye jama'arsa,Yakan kiyaye sarkinsa da ya zaɓa, ya kuma cece shi.

9. Ka ceci jama'arka, ya Ubangiji,Ka sa wa waɗanda suke naka albarka!Ka zama makiyayinsu,Ka lura da su har abada.

Karanta cikakken babi Zab 28