Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 26:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ya Ubangiji, ina ƙaunar Haikali inda zatinka yake,Inda ɗaukakarka yake zaune.

9. Kada ka hallaka ni tare da masu zunubi,Ka cece ni daga ƙaddarar masu kisankai,

10. Mutanen da suke aikata mugunta a dukan lokaci,A koyaushe suna shirye don su ba da rashawa.

11. Amma ni, ina yin abin da yake daidai,Ka yi mini jinƙai ka fanshe ni!

12. Na kuɓuta daga dukan hatsarori,A taron sujada na yabi Ubangiji!

Karanta cikakken babi Zab 26