Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 26:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka hurta rashin laifina, ya Ubangiji,Gama na yi abin da suke daidai,Na dogara gare ka gaba ɗaya.

2. Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji,Ka gwada muradina da tunanina.

3. Madawwamiyar ƙaunarka tana bi da ni,Amincinka yake yi mini jagora kullayaumin.

4. Ba na tarayya da mutanen banza,Ba abin da ya gama ni da masu riya.

5. Ina ƙin tarayya da masu mugunta,Nakan kauce wa mugaye.

Karanta cikakken babi Zab 26