Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 25:3-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Waɗanda suke dogara gare ka,Ba za su kasa yin nasara ba,Sai dai waɗanda suke gaggawa su yi maka tayarwa.

4. Ka koya mini al'amuranka, ya Ubangiji,Ka sa su zama sanannu a gare ni.

5. Ka koya mini in yi zamana bisa ga gaskiyarka,Gama kai Mai Cetona ne.Dukan yini ina dogara a gare ka.

6. Ya Ubangiji, ka tuna da alherinka da madawwamiyar ƙaunarka,Waɗanda ka nuna tun a dā.

7. Ka gafarta zunubaina da kurakuraina masu yawa na ƙuruciyata.Saboda madawwamiyar ƙaunarka da alherinka,Ka tuna da ni, ya Ubangiji!

8. Ubangiji mai adalci ne, mai alheri,Yana koya wa masu zunubi tafarkin da za su bi.

9. Yana bi da masu tawali'u a tafarkin da suke daidai,Yana koya musu nufinsa.

10. Da ƙauna da aminci yana bi da dukan waɗanda suke biyayya da alkawarinsa da umarnansa.

11. Ka cika alkawarinka, ya Ubangiji, ka gafarta zunubaina, gama suna da yawa.

12. Waɗanda suke biyayya da UbangijiZa su koyi hanyar da za su bi daga gare shi.

13. Kullayaumi za su arzuta,'Ya'yansu kuma za su zauna lafiya a ƙasar.

14. Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi,Yakan koya musu alkawarinsa.

15. A koyaushe ga Ubangiji nake neman taimako,Yakan kuɓutar da ni daga hatsari.

16. Ka juyo wajena, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai,Gama ina zaman kaɗaici da rashin ƙarfi.

Karanta cikakken babi Zab 25