Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 25:10-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Da ƙauna da aminci yana bi da dukan waɗanda suke biyayya da alkawarinsa da umarnansa.

11. Ka cika alkawarinka, ya Ubangiji, ka gafarta zunubaina, gama suna da yawa.

12. Waɗanda suke biyayya da UbangijiZa su koyi hanyar da za su bi daga gare shi.

13. Kullayaumi za su arzuta,'Ya'yansu kuma za su zauna lafiya a ƙasar.

14. Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi,Yakan koya musu alkawarinsa.

15. A koyaushe ga Ubangiji nake neman taimako,Yakan kuɓutar da ni daga hatsari.

16. Ka juyo wajena, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai,Gama ina zaman kaɗaici da rashin ƙarfi.

17. Damuwar zuciyata ta yi yawa,Ka raba ni da dukan damuwa,Ka cece ni daga dukan wahalata.

18. Ka kula da wahalata da azabata,Ka gafarta dukan zunubaina.

19. Ka duba yawan magabtan da nake da su,Dubi irin ƙiyayyar da suke yi mini!

20. Ka yi mini kāriya, ka cece ni,Gama na zo wurinka neman kāriya.

21. Ka sa nagartata da amincina su kiyaye ni,Gama na dogara gare ka.

22. Ka fanshi jama'arka daga dukan wahalarsu, ya Allah!

Karanta cikakken babi Zab 25