Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 23:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji makiyayina ne,Ba zan rasa kome ba.

2. Yana sa ni in huta a saura mai ɗanyar ciyawa,Yana bi da ni a tafkuna masu daɗin ruwa, suna kwance lif.

3. Yana ba ni sabon ƙarfi.Yana bi da ni a hanyar da suke daidai kamar yadda ya alkawarta.

4. Ko da hanyan nan ta bi ta tsakiyar duhu na mutuwa,Ba zan ji tsoro ba, ya Ubangiji,Gama kana tare da ni!Sandanka na makiyayi da kerenkaSuna kiyaye lafiyata.

5. Ka shirya mini liyafaInda maƙiyana duk za su iya ganina,Ka marabce ni, ka shafe kaina da mai,Ka cika tanduna fal da mai.

6. Hakika, alherinka da ƙaunarkaZa su kasance tare da ni muddin raina.Haikalinka zai zama gidana har abada.

Karanta cikakken babi Zab 23