Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 18:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Hayaƙi ya yi ta tuƙaƙowa daga hancinsa,Harshen wuta da garwashi suna fitowa daga bakinsa.

9. Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa,Tare da girgije mai duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa.

10. Ya sauko ta bisa bayan kerubobi,Yana tafe da sauri a kan fikafikan iska.

11. Ya rufe kansa da duhu,Gizagizai masu duhu cike da ruwa, suna kewaye da shi.

12. Ƙanƙara da garwashin wuta suka saukoDaga cikin walƙiya da take gabansa,Suka keto ta cikin gizagizai masu duhu.

13. Sa'an nan Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama,Aka ji muryar Maɗaukaki.Ƙanƙara da garwashin wuta suka sauko.

14. Ya harba kibansa, ya watsa magabtana,Da walƙatawar walƙiya ya kore su.

15. Kashiyar teku ta bayyana,Tussan duniya sun bayyana,Sa'ad da ka tsauta wa magabtana, ya Ubangiji,Sa'ad da kuma ka yi musu tsawa da fushi.

16. Ubangiji ya miƙa hannunsa daga samaniya ya ɗauke ni,Ya tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi.

17. Ya cece ni daga magabtana masu ƙarfi,Daga kuma dukan masu ƙina,Gama sun fi ƙarfina!

18. Sa'ad da nake shan wahala suka auka mini,Amma Ubangiji ya kiyaye ni.

Karanta cikakken babi Zab 18