Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 18:32-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Shi ne Allahn da yake ƙarfafa ni,Yana kiyaye lafiyata a kan hanya.

33. Yana sa in tabbata lafiya nake tafiya, kamar barewa.Yana kiyaye ni lafiya a kan duwatsu.

34. Yakan horar da ni don yaƙi,Domin in iya amfani da baka mafi ƙarfi.

35. Ya Ubangiji ka kiyaye ni, ka cece ni,Na zama babban mutum saboda kana lura da ni,Ikonka kuma ya kiyaye lafiyata.

36. Ka tsare ni, ba a kama ni ba,Ban kuwa taɓa fāɗuwa ba.

37. Na kori magabtana, har na kama su,Ba zan tsaya ba, sai na yi nasara da su.

38. Zan buge su har ƙasa, ba kuwa za su tashi ba,Za su fāɗi ƙarƙashin ƙafafuna.

39. Kakan ba ni ƙarfin yin yaƙi,Kakan ba ni nasara a kan magabtana.

Karanta cikakken babi Zab 18