Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 18:25-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Kai, ya Ubangiji, mai aminci ne ga masu aminci,Kai nagari ne, cikakke ga kamilai.

26. Kai Mai Tsarki ne ga waɗanda suke tsarkaka,Amma kana gāba da mugaye.

27. Kakan ceci masu tawali'u,Amma kakan ƙasƙantar da masu girmankai.

28. Ubangiji yakan ba ni haske,Allah yakan kawar da duhuna.

29. Yakan ba ni ƙarfin da zan fāɗa wa magabtana,Da ikon rinjayar kagararsu.

30. Wannan Allah dai! Ayyukansa kamiltattu ne ƙwarai,Maganarsa abar dogara ce!Kamar garkuwa yake, ga duk mai neman taimako a wurinsa.

31. Ubangiji shi kaɗai ne Allah,Allah ne kaɗai kāriyamu.

32. Shi ne Allahn da yake ƙarfafa ni,Yana kiyaye lafiyata a kan hanya.

33. Yana sa in tabbata lafiya nake tafiya, kamar barewa.Yana kiyaye ni lafiya a kan duwatsu.

34. Yakan horar da ni don yaƙi,Domin in iya amfani da baka mafi ƙarfi.

35. Ya Ubangiji ka kiyaye ni, ka cece ni,Na zama babban mutum saboda kana lura da ni,Ikonka kuma ya kiyaye lafiyata.

36. Ka tsare ni, ba a kama ni ba,Ban kuwa taɓa fāɗuwa ba.

37. Na kori magabtana, har na kama su,Ba zan tsaya ba, sai na yi nasara da su.

Karanta cikakken babi Zab 18