Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 18:14-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ya harba kibansa, ya watsa magabtana,Da walƙatawar walƙiya ya kore su.

15. Kashiyar teku ta bayyana,Tussan duniya sun bayyana,Sa'ad da ka tsauta wa magabtana, ya Ubangiji,Sa'ad da kuma ka yi musu tsawa da fushi.

16. Ubangiji ya miƙa hannunsa daga samaniya ya ɗauke ni,Ya tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi.

17. Ya cece ni daga magabtana masu ƙarfi,Daga kuma dukan masu ƙina,Gama sun fi ƙarfina!

18. Sa'ad da nake shan wahala suka auka mini,Amma Ubangiji ya kiyaye ni.

19. Ya fisshe ni daga cikin hatsari,Ya cece ni, don yana jin daɗina.

20. Ubangiji yakan sāka mini, saboda ni adali ne,Yakan sa mini albarka, don ni marar laifi ne.

21. Na yi biyayya da umarnan Ubangiji,Ban yi wa Ubangiji Allahna tawaye ba.

22. Na kiyaye dukan dokokinsa,Ban yi rashin biyayya da umarnansa ba.

23. Ya sani ba ni da laifi,Domin na kiyaye kaina daga mugunta.

24. Don haka ya sāka mini, domin ni adali ne,Gama ya sani ni marar laifi ne.

25. Kai, ya Ubangiji, mai aminci ne ga masu aminci,Kai nagari ne, cikakke ga kamilai.

Karanta cikakken babi Zab 18