Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 18:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ina ƙaunarka ƙwarai, ya Ubangiji!Kai ne mai kāre ni.

2. Ubangiji ne Mai Cetona,Shi ne garkuwata mai ƙarfi.Allahna, shi ne yake kiyaye ni,Lafiya nake sa'ad da nake tare da shi,Yana kiyaye ni kamar garkuwa,Yana kāre ni, ya ba ni lafiya.

3. Na yi kira ga Ubangiji,Yakan cece ni daga magabtana,Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

4. Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta,Halaka ta auko mini a kai a kai.

5. Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta,Kabari kuma ya ɗana mini tarko.

Karanta cikakken babi Zab 18