Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 150:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Ku yabi Allah a cikin Haikalinsa!Ku yabi ƙarfinsa a sama!

2. Ku yabe shi saboda manyan abubuwaWaɗanda ya aikata!Ku yabi mafificin girmansa!

3. Ku yabe shi da kakaki!Ku yabe shi da garayu da molaye!

4. Ku yabe shi da bandiri kuna taka rawa!Ku yabe shi da garayu da sarewa!

5. Ku yabe shi da kuge!Ku yabe shi da kuge masu amo!

6. Ku yabi Ubangiji dukanku rayayyun talikai.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Karanta cikakken babi Zab 150