Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 149:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Ku raira sabuwar waƙa ga UbangijiKu yabe shi cikin taron jama'arsa masu aminci!

2. Ki yi murna, ke Isra'ila, sabili da Mahaliccinki,Ku yi farin ciki, ku jama'ar Sihiyona, sabili da Sarkinku!

3. Ku yabi sunansa, kuna taka rawa,Ku kaɗa bandiri da garayu, kuna yabonsa.

4. Ubangiji yana jin daɗin jama'arsa,Yakan girmama mai tawali'u ya sa ya ci nasara.

Karanta cikakken babi Zab 149