Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 148:9-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ku yabe shi, ku tuddai da duwatsu,Da itatuwa 'ya'ya da kurama.

10. Ku yabe shi dukanku dabbobi, na gida da na jeji,Masu rarrafe da tsuntsaye!

11. Ku yabe shi, ku sarakuna da dukan kabilai,Ku yabe shi, ku shugabanni da dukan hukumomi.

12. Ku yabe shi ku samari da 'yan mata!Ku yabe shi, ku tsoffafi da yara!

13. Bari dukansu su yabi sunan Ubangiji,Sunansa ya fi dukan sauran sunaye girma,ĆŠaukakarsa kuwa tana bisa duniya da samaniya!

Karanta cikakken babi Zab 148