Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 148:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ta wurin umarninsa aka kafa suA wurarensu har abada,Ba su kuwa da ikon ƙi.

7. Ku yabi Ubangiji daga duniya,Ku yabi Ubangiji, ku dodanin ruwa da dukan zurfafan teku.

8. Ku yabe shi, ku walƙiya, da ƙanƙara, da dusar ƙanƙara,Da gizagizai, da ƙarfafan iska waɗanda suke biyayya da umarnansa!

9. Ku yabe shi, ku tuddai da duwatsu,Da itatuwa 'ya'ya da kurama.

10. Ku yabe shi dukanku dabbobi, na gida da na jeji,Masu rarrafe da tsuntsaye!

11. Ku yabe shi, ku sarakuna da dukan kabilai,Ku yabe shi, ku shugabanni da dukan hukumomi.

12. Ku yabe shi ku samari da 'yan mata!Ku yabe shi, ku tsoffafi da yara!

13. Bari dukansu su yabi sunan Ubangiji,Sunansa ya fi dukan sauran sunaye girma,Ɗaukakarsa kuwa tana bisa duniya da samaniya!

14. Ya sa al'ummarsa ta yi ƙarfi,Domin dukan jama'arsa su yabe shiJama'arsa Isra'ila, wadda yake ƙauna ƙwarai!Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Karanta cikakken babi Zab 148