Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 148:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Ku yabi Ubangiji daga sama,Ku da kuke zaune a tuddan sama.

2. Ku yabe shi dukanku mala'ikunsa,Ku yabe shi, ku dukan rundunansa na sama!

3. Ku yabe shi, ku rana da wata,Ku yabe shi, ku taurari masu haskakawa!

4. Ku yabe shi, ku sammai mafi tsayi duka!Ku yabe shi, ku ruwayen da kuke bisa sararin sama!

5. Bari su duka su yabi sunan Ubangiji!Ya umarta, sai suka kasance.

6. Ta wurin umarninsa aka kafa suA wurarensu har abada,Ba su kuwa da ikon ƙi.

7. Ku yabi Ubangiji daga duniya,Ku yabi Ubangiji, ku dodanin ruwa da dukan zurfafan teku.

8. Ku yabe shi, ku walƙiya, da ƙanƙara, da dusar ƙanƙara,Da gizagizai, da ƙarfafan iska waɗanda suke biyayya da umarnansa!

Karanta cikakken babi Zab 148