Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 140:8-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ya Ubangiji, kada ka biya wa mugaye burinsu,Kada ka bar mugayen dabaru su yi nasara!

9. “Kada ka bar maƙiyana su sami nasara,Ka sa kashedin da suke yi mini yă koma kansu.

10. Ka sa garwashin wuta yă zubo a kansu,Ka sa a jefa su a rami, kada su ƙara fita.

11. Ka sa waɗanda suke saran waɗansu a ƙaryace,Kada su yi nasara.Ka sa mugunta ta hallaka mutumin da yake ta da zaune tsaye.”

12. Na sani kai, ya Ubangiji, kana kāre matsalar talakawa,Da hakkin matalauta.

13. Hakika adalai za su yabe ka,Za su zauna a gabanka.

Karanta cikakken babi Zab 140