Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 138:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da zuciya ɗaya nake gode maka, ya Ubangiji,Ina raira waƙar yabonka a gaban alloli.

2. Na durƙusa a gaban tsattsarkan HaikalinkaIna yabon sunanka.Sabili da madawwamiyar ƙaunarka da amincinka,Saboda ka nuna ɗaukakarka da umarnanka.

3. Ka amsa mini sa'ad da na yi kira gare ka,Da ƙarfinka ka ƙarfafa ni.

4. Dukan sarakunan duniyar nan za su yabe ka, ya Ubangiji,Gama sun riga sun ji alkawaranka.

5. Za su raira waƙa a kan abin da Ubangiji ya yi,Za su raira waƙa kuma a kan ɗaukakarsa mai girma.

6. Ko da yake Ubangiji yana can Sama,Duk da haka yana kulawa da masu kaɗaici.Masu girmankai kuwa ba za su iya ɓoye kansu daga gare shi ba.

7. Ko lokacin da nake tsakiyar wahala,Za ka kiyaye ni lafiya,Ka yi gāba da abokan gābana, waɗanda suka husata,Za ka kuwa cece ni da ikonka.

8. Za ka aikata kowane abu da ka alkawarta mini,Ya Ubangiji, ƙaunarka madawwamiya ce har abada.Ka cikasa aikin da ka fara.

Karanta cikakken babi Zab 138