Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 137:2-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. A rassan itatuwan wardi da suke kusa da muMuka rataye garayunmu.

3. Waɗanda suka kama mu suka sa mu mu yi waƙa,Suka ce mana, “Ku yi mana shagaliDa waƙar da aka raira wa Sihiyona!”

4. Kaƙa za mu raira waƙar UbangijiA baƙuwar ƙasa?

5. Da ma kada in ƙara iya kaɗa garaya,Idan na manta da ke, Urushalima!

6. Da ma kada in ƙara iya raira waƙa,Idan na manta da ke,Idan ban tuna ke ceBabbar abar farin ciki ba!

7. Ka tuna, ya Ubangiji, da abin da Edomawa suka yi,A ranar da aka ci Urushalima.Ka tuna da yadda suka ce,“A ragargaza ta har ƙasa!”

8. Babila, za a hallaka ki!Mai farin ciki ne shi wanda ya sāka mikiBisa ga abin da kika yi mana.

9. Mai farin ciki ne shi wanda zai kwashi jarirankiYă fyaɗa su a kan duwatsu!

Karanta cikakken babi Zab 137