Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 136:6-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ya kafa duniya a bisa kan ruwa mai zurfi,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

7. Shi ne ya halicci rana da wata,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,

8. Rana don ta yi mulkin yini,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,

9. Wata da taurari kuwa don su yi mulkin dare,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

10. Shi ya karkashe 'ya'yan fari maza, na Masarawa,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

11. Shi ya fito da jama'ar Isra'ila daga cikin Masar,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

12. Da ƙarfinsa da ikonsa ya fito da su,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

13. Shi ne ya keta Bahar Maliya biyu,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

14. Shi ya bi da jama'arsa ta cikin tekun,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

15. Shi ne ya sa ruwa ya ci Fir'auna da rundunarsa,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

16. Ya bi da jama'arsa cikin hamada,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

Karanta cikakken babi Zab 136