Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 136:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku gode wa Ubangiji domin shi mai alheri ne,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

2. Ku gode wa Allahn da ya fi dukan alloli girma,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

3. Ku gode wa Ubangijin dukan iyayengiji,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

4. Shi kaɗai ne yake aikata mu'ujizai masu girma,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

5. Ta wurin hikimarsa ya halicci sammai,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

6. Ya kafa duniya a bisa kan ruwa mai zurfi,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

7. Shi ne ya halicci rana da wata,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,

8. Rana don ta yi mulkin yini,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,

Karanta cikakken babi Zab 136