Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 130:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A cikin fid da zuciyata,Na yi kira gare ka, ya Ubangiji.

2. Ka ji kukana, ya Ubangiji,Ka kasa kunne ga kiran da nake yi na neman taimako!

3. Idan kana yin lissafin zunubanmu,Wa zai kuɓuta daga hukunci?

4. Amma kakan gafarta mana,Domin mu zama masu tsoronka.

5. Na zaƙu, ina jiran taimako daga Ubangiji,Ga maganarsa na dogara.

6. Ina jiran Ubangiji,Na zaƙu ƙwarai, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir,I, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir.

7. Ya Isra'ila, ki dogara ga Ubangiji,Saboda ƙaunarsa madawwamiya ce,A koyaushe yana da nufin yin gafara.

8. Zai fanshi jama'arsa Isra'ilaDaga dukan zunubansu.

Karanta cikakken babi Zab 130