Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 129:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Isra'ila, sai ka faɗi irin muguntarDa maƙiyanka suka tsananta maka da ita,Tun kana ƙarami!

2. “Maƙiyana suka tsananta mini da mugunta,Tun ina ƙarami,Amma ba su yi nasara da ni ba.

3. Suka sa mini raunuka masu zurfi a bayana,Suka mai da shi kamar gonar da aka nome.

4. Amma Ubangiji mai adalci,Ya 'yantar da ni daga bauta.”

5. Allah ya sa duk waɗanda suke ƙin Sihiyona,A yi nasara da su a kuma kore su!

6. Allah ya sa su zama kamar ciyawar da take girma a kan soraye,Ta kuwa bushe kafin ta isa yanka.

Karanta cikakken babi Zab 129