Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 122:4-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. A nan kabilai sukan zo,Kabilan Isra'ila,Domin su yi godiya ga Ubangiji,Kamar yadda ya umarce su.

5. A nan majalisu suke,Wurin da sarki yake yi wa jama'arsa shari'a.

6. Ku yi wa Urushalima addu'ar salama!“Allah ya sa masu ƙaunarki su arzuta!

7. Salama ta samu a garukanki,Da zaman lafiya kuma a fādodinki.”

8. Saboda abokaina da aminaina,Na ce wa Urushalima, “Salama a gare ki!”

9. Saboda Haikalin Ubangiji, Allahnmu,Ina addu'a domin ki arzuta.

Karanta cikakken babi Zab 122