Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 121:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na duba wajen duwatsu,Daga ina taimakona zai zo?

2. Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,Wanda ya yi sama da ƙasa.

3. Ba zai bar ka ka fāɗi ba,Makiyayinka, ba zai yi barci ba!

4. Makiyayin Isra'ila,Ba ya gyangyaɗi ko barci!

5. Ubangiji zai lura da kai,Yana kusa da kai domin ya kiyaye ka.

6. Ba za ka sha rana ba,Ko farin wata da dare.

7. Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan hatsari,Zai sa ka zauna lafiya.

Karanta cikakken babi Zab 121