Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 12:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka cece ni, ya Ubangiji,Ba sauran mutanen kirki,Ba kuma za a sami amintattun mutane ba.

2. Dukan mutane suna yi wa juna ƙarya,Suna ruɗin junansu da yaudara.

3. Ka sa harsunan nan masu yaudara su yi shiru,Ya Ubangiji, ka rufe bakunan nan masu fāriya!

4. Sukan ce, “Za mu yi magana yadda muka ga dama,Ba kuwa wanda zai hana mu.Wane ne yake da ikon faɗa mana abin da za mu faɗa?”

5. Ubangiji ya ce, “Amma zan zo yanzu,Domin ana zaluntar masu bukata,Waɗanda aka tsananta musu kuma, suna nishi don zafi.Zan ba su zaman lafiya da suke nema!”

6. Alkawaran Ubangiji abin dogara ne,Alkawarai ne na ainihi kamar azurfaDa aka tace har sau bakwai cikin matoya.

7. Ka kiyaye lafiyarmu, ya Ubangiji,Ka kiyaye mu daga irin waɗannan mutane.

8. Akwai mugaye ko'ina, suna ta yanga,Suna ta yabon abin da yake mugunta.

Karanta cikakken babi Zab 12