Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:98-108 Littafi Mai Tsarki (HAU)

98. Umarninka yana tare da ni a kowane lokaci,Ya sa ni in yi hikima fiye da dukan maƙiyana.

99. Ganewata ta fi ta dukan malamaina,Saboda ina ta tunani a kan koyarwarka.

100. Na fi tsofaffi hikima,Saboda ina biyayya da umarnanka.

101. Nakan guje wa halin muguntaSaboda ina so in yi biyayya da maganarka.

102. Ban raina koyarwarka baSaboda kai ne ka koya mini.

103. Ɗanɗanon ka'idodinka akwai zaƙi,Har sun fi zuma zaƙi!

104. Na ƙaru da hikima daga dokokinka,Saboda haka ina ƙin dukan halin da yake ba daidai ba.

105. Maganarka fitila ce wadda za ta bi da ni,Haske ne kuma a kan hanyata.

106. Zan cika muhimmin alkawarina,In yi biyayya da koyarwarka mai adalci.

107. Azabaina, ya Ubangiji, suna da yawa,Ka rayar da ni kamar yadda ka alkawarta!

108. Ka karɓi addu'ata ta godiya, ya Ubangiji,Ka koya mini umarnanka.

Karanta cikakken babi Zab 119