Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:94-105 Littafi Mai Tsarki (HAU)

94. Ni naka ne, ka cece ni!Na yi ƙoƙari in yi biyayya da umarnanka.

95. Mugaye suna jira su kashe ni,Amma zan yi ta tunani a kan dokokinka.

96. Na koya cewa ba wani abu da yake cikakke,Amma umarninka ba shi da iyaka.

97. Ga yadda nake ƙaunar dokarka!Ina ta tunani a kanta dukan yini.

98. Umarninka yana tare da ni a kowane lokaci,Ya sa ni in yi hikima fiye da dukan maƙiyana.

99. Ganewata ta fi ta dukan malamaina,Saboda ina ta tunani a kan koyarwarka.

100. Na fi tsofaffi hikima,Saboda ina biyayya da umarnanka.

101. Nakan guje wa halin muguntaSaboda ina so in yi biyayya da maganarka.

102. Ban raina koyarwarka baSaboda kai ne ka koya mini.

103. Ɗanɗanon ka'idodinka akwai zaƙi,Har sun fi zuma zaƙi!

104. Na ƙaru da hikima daga dokokinka,Saboda haka ina ƙin dukan halin da yake ba daidai ba.

105. Maganarka fitila ce wadda za ta bi da ni,Haske ne kuma a kan hanyata.

Karanta cikakken babi Zab 119