Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:87-95 Littafi Mai Tsarki (HAU)

87. Sun kusa ci wa burinsu na su kashe ni,Amma ban raina ka'idodinka ba.

88. Saboda madawwamiyar ƙaunarka, ka yi mini alheri,Domin in yi biyayya da dokokinka.

89. Maganarka tabbatacciya ce, ya Ubangiji,A kafe take a Sama.

90. Amincinka ya tabbata har abada,Ka kafa duniya a inda take, tana nan kuwa a wurin.

91. Dukan abubuwa suna nan har wa yau saboda umarninka,Domin su duka bayinka ne.

92. Da ba domin dokarka ita ce sanadin farin cikina ba,Da na mutu saboda hukuncin da na sha.

93. Faufau ba zan raina ka'idodinka ba,Gama saboda su ka bar ni da rai.

94. Ni naka ne, ka cece ni!Na yi ƙoƙari in yi biyayya da umarnanka.

95. Mugaye suna jira su kashe ni,Amma zan yi ta tunani a kan dokokinka.

Karanta cikakken babi Zab 119