Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:74-84 Littafi Mai Tsarki (HAU)

74. Waɗanda suke tsoronka za su yi murna sa'ad da suka gan ni,Saboda ina dogara ga alkawarinka.

75. Na sani ka'idodinka na adalci ne, ya Ubangiji,Ka hore ni, domin kai mai aminci ne.

76. Ka sa madawwamiyar ƙaunarka ta ta'azantar da ni,Kamar yadda ka alkawarta mini, ni bawanka.

77. Ka yi mini jinƙai, zan rayu,Saboda ina murna da dokarka.

78. Ka kunyatar da masu girmankaiSaboda sun ba da shaidar zur a kaina,Amma ni, zan yi tunani a kan ka'idodinka.

79. Ka sa waɗanda suke tsoronka su zo gare ni,Da waɗanda suka san umarnanka.

80. Ka sa in yi cikakkiyar biyayya da umarnanka,Sa'an nan zan tsere wa shan kunyar faɗuwa.

81. Na tafke, ya Ubangiji, jira nake ka cece ni,Na dogara ga maganarka.

82. Idanuna sun gaji da zuba ido ga alkawarinka.Roƙo nake, “Sai yaushe za ka taimake ni?”

83. Na zama marar amfani kamar salkar ruwan inabi wanda aka jefar da ita,Duk da haka ban manta da umarnanka ba.

84. Har yaushe zan yi ta jira?Yaushe za ka yi wa waɗanda suke tsananta mini hukunci?

Karanta cikakken babi Zab 119