Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:60-75 Littafi Mai Tsarki (HAU)

60. Ba tare da ɓata lokaci ba,Zan gaggauta in kiyaye umarnanka.

61. Mugaye sun ɗaure ni tam da igiyoyi,Amma ba zan manta da dokarka ba.

62. Da tsakar dare nakan farka,In yabe ka saboda hukuntanka masu adalci.

63. Ina abuta da duk waɗanda suke bauta maka,Da duk waɗanda suke kiyaye dokokinka.

64. Ya Ubangiji, duniya ta cika da madawwamiyar ƙaunarka,Ka koya mini umarnanka!

65. Kana cika alkawarinka, ya Ubangiji,Kana kuwa yi mini alheri, ni bawanka.

66. Ka ba ni hikima da ilimiDomin ina dogara ga umarnanka.

67. Kafin ka hore ni nakan yi kuskure,Amma yanzu ina biyayya da maganarka.

68. Managarci ne kai, mai alheri ne kuma,Ka koya mini umarnanka!

69. Masu girmankai sun faɗi ƙarairayi a kaina,Amma da zuciya ɗaya nake biyayya da ka'idodinka.

70. Waɗannan mutane ba su da ganewa,Amma ni ina murna da dokarka.

71. Horon da aka yi mini ya yi kyau,Domin ya sa na koyi umarnanka.

72. Dokar da ka yiMuhimmiya ce a gare ni,Fiye da dukan dukiyar duniya.

73. Kai ne ka halicce ni, ka kuma kiyaye ni lafiya,Ka ba ni ganewa, don in koyi dokokinka.

74. Waɗanda suke tsoronka za su yi murna sa'ad da suka gan ni,Saboda ina dogara ga alkawarinka.

75. Na sani ka'idodinka na adalci ne, ya Ubangiji,Ka hore ni, domin kai mai aminci ne.

Karanta cikakken babi Zab 119