Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:53-59 Littafi Mai Tsarki (HAU)

53. Haushi ya kama ni sosai,Sa'ad da na ga mugaye suna keta dokarka.

54. Ina zaune can nesa da gidana na ainihi,Sai na ƙago waƙoƙi a kan umarnanka.

55. Da dare nakan tuna da kai, ya Ubangiji,Ina kuwa kiyaye dokarka.

56. Wannan shi ne farin cikina,In yi biyayya da umarnanka.

57. Kai kaɗai nake so, ya Ubangiji,Na yi alkawari in yi biyayya da dokokinka.

58. Ina roƙonka da zuciya ɗaya,Ka yi mini jinƙai kamar yadda ka alkawarta!

59. Na yi tunani a kan ayyukana,Na yi alkawari in bi ka'idodinka.

Karanta cikakken babi Zab 119