Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:50-58 Littafi Mai Tsarki (HAU)

50. Ko ina shan wahala, ana ta'azantar da ni,Saboda alkawarinka yana rayar da ni.

51. Masu girmankai suna raina ni,Amma ban rabu da dokarka ba.

52. Na tuna da koyarwar da ka yi mini a dā,Sukan kuwa ta'azantar da ni, ya Ubangiji.

53. Haushi ya kama ni sosai,Sa'ad da na ga mugaye suna keta dokarka.

54. Ina zaune can nesa da gidana na ainihi,Sai na ƙago waƙoƙi a kan umarnanka.

55. Da dare nakan tuna da kai, ya Ubangiji,Ina kuwa kiyaye dokarka.

56. Wannan shi ne farin cikina,In yi biyayya da umarnanka.

57. Kai kaɗai nake so, ya Ubangiji,Na yi alkawari in yi biyayya da dokokinka.

58. Ina roƙonka da zuciya ɗaya,Ka yi mini jinƙai kamar yadda ka alkawarta!

Karanta cikakken babi Zab 119