Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:40-50 Littafi Mai Tsarki (HAU)

40. Ina so in yi biyayya da umarnanka,Gama kai mai adalci ne,Ka yi mini alheri!

41. Ka nuna mini yawan ƙaunar da kake yi mini, ya Ubangiji,Ka cece ni bisa ga alkawarinka.

42. Sa'an nan zan amsa wa waɗanda suke cin mutuncina,Domin na dogara ga maganarka.

43. Ka ba ni iko in iyar da saƙonka na gaskiya a kowane lokaci,Gama sa zuciyata tana ga hukuntanka.

44. Kullum zan yi biyayya da dokarka har abada abadin!

45. Zan rayu da cikakken 'yanci,Gama na yi ƙoƙari in kiyaye ka'idodinka.

46. Zan hurta umarnanka ga sarakuna,Ba kuwa zan ji kunya ba.

47. Ina murna in yi biyayya da umarnanka,Saboda in ƙaunarsu.

48. Ina girmama umarnanka, ina kuwa ƙaunarsu,Zan yi ta tunani a kan koyarwarka.

49. Ka tuna da alkawarin da ka yi mini, ni bawanka,Ka ƙarfafa zuciyata.

50. Ko ina shan wahala, ana ta'azantar da ni,Saboda alkawarinka yana rayar da ni.

Karanta cikakken babi Zab 119