Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:4-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Kai ka ba mu dokokinka,Ka kuwa faɗa mana mu kiyaye su da aminci.

5. Na sa zuciya zan yi aminci,Game da kiyaye dokokinka!

6. Idan na kula da dukan umarnanka,To, ba zan kasa kaiwa ga burina ba.

7. Zan yabe ka da tsattsarkar zuciya,A sa'ad da na fahimci ka'idodinka masu adalci.

8. Zan yi biyayya da dokokinka,Ko kusa kada ka kashe ni!

9. Ƙaƙa saurayi zai kiyaye ransa da tsarki?Sai ta wurin biyayya da umarnanka.

10. Da zuciya ɗaya nake ƙoƙarin bauta maka,Ka kiyaye ni daga rashin biyayya da umarnanka!

11. Na riƙe maganarka a zuciyata,Don kada in yi maka zunubi.

12. Ina yabonka, Ya Ubangiji,Ka koya mini ka'idodinka!

Karanta cikakken babi Zab 119