Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:3-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Hakika ba su yin laifi,Sukan yi tafiya a hanyoyin Ubangiji.

4. Kai ka ba mu dokokinka,Ka kuwa faɗa mana mu kiyaye su da aminci.

5. Na sa zuciya zan yi aminci,Game da kiyaye dokokinka!

6. Idan na kula da dukan umarnanka,To, ba zan kasa kaiwa ga burina ba.

7. Zan yabe ka da tsattsarkar zuciya,A sa'ad da na fahimci ka'idodinka masu adalci.

8. Zan yi biyayya da dokokinka,Ko kusa kada ka kashe ni!

9. Ƙaƙa saurayi zai kiyaye ransa da tsarki?Sai ta wurin biyayya da umarnanka.

10. Da zuciya ɗaya nake ƙoƙarin bauta maka,Ka kiyaye ni daga rashin biyayya da umarnanka!

11. Na riƙe maganarka a zuciyata,Don kada in yi maka zunubi.

12. Ina yabonka, Ya Ubangiji,Ka koya mini ka'idodinka!

13. Zan ta da murya,In maimaita dukan dokokin da ka bayar.

14. Ina murna da bin umarnanka,Fiye da samun dukiya mai yawa.

15. Nakan yi nazarin umarnanka,Nakan kuma yi bimbinin koyarwarka.

Karanta cikakken babi Zab 119