Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:27-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Ka koya mini yadda zan yi biyayya da dokokinka,In kuma yi nazarin koyarwarka mai banmamaki.

28. Ɓacin rai ya ci ƙarfina,Ka ƙarfafa ni, kamar yadda ka alkawarta.

29. Ka kiyaye ni daga bin muguwar hanya,Ta wurin alherinka, ka koya mini dokarka.

30. Na yi niyya in yi biyayya,Na mai da hankali ga ka'idodinka.

31. Na bi umarnanka, ya Ubangiji,Kada ka sa in kasa ci wa burina!

32. Ina ɗokin yin biyayya da umarnanka,Gama za ka ƙara mini fahimi.

33. Ka koya mini ma'anar dokokinka, ya Ubangiji,Zan kuwa yi biyayya da su a kowane lokaci.

34. Ka fassara mini dokarka, ni kuwa zan yi biyayya da ita,Zan kiyaye ta da zuciya ɗaya.

35. Ka bishe ni a hanyar umarnanka,Domin a cikinsu nakan sami farin ciki

36. Ka sa ni in so yin biyayya da ka'idodinka,Fiye da samun dukiya.

37. Ka kiyaye ni daga mai da hankali ga abin da yake marar amfani,Ka yi mini alheri kamar yadda ka alkawarta.

38. Ka tabbatar da alkawarin da ka yi mini, ni bawanka,Irin wanda kakan yi wa waɗanda suke tsoronka.

39. Ka kiyaye ni daga cin mutuncin da nake tsoro,Ka'idodinka suna da amfani ƙwarai!

40. Ina so in yi biyayya da umarnanka,Gama kai mai adalci ne,Ka yi mini alheri!

Karanta cikakken babi Zab 119