Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:24-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Umarnanka suna faranta mini rai,Su ne mashawartana.

25. Ina kwance cikin ƙura, an yi nasara da ni,Ka wartsakar da ni kamar yadda ka alkawarta!

26. Na hurta dukan abin da na aikata, ka kuwa amsa mini,Ka koya mini ka'idodinka!

27. Ka koya mini yadda zan yi biyayya da dokokinka,In kuma yi nazarin koyarwarka mai banmamaki.

28. Ɓacin rai ya ci ƙarfina,Ka ƙarfafa ni, kamar yadda ka alkawarta.

29. Ka kiyaye ni daga bin muguwar hanya,Ta wurin alherinka, ka koya mini dokarka.

30. Na yi niyya in yi biyayya,Na mai da hankali ga ka'idodinka.

31. Na bi umarnanka, ya Ubangiji,Kada ka sa in kasa ci wa burina!

32. Ina ɗokin yin biyayya da umarnanka,Gama za ka ƙara mini fahimi.

33. Ka koya mini ma'anar dokokinka, ya Ubangiji,Zan kuwa yi biyayya da su a kowane lokaci.

34. Ka fassara mini dokarka, ni kuwa zan yi biyayya da ita,Zan kiyaye ta da zuciya ɗaya.

Karanta cikakken babi Zab 119