Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:171-176 Littafi Mai Tsarki (HAU)

171. Zan yabe ka kullayauminDomin ka koya mini ka'idodinka.

172. Zan raira waƙa a kan alkawarinka,Domin umarnanka a gaskiya ne.

173. Kullum a shirye kake domin ka taimake ni,Saboda ina bin umarnanka.

174. Ina sa zuciya ga cetonka ƙwarai, ya Ubangiji!Ina samun farin ciki ga dokarka.

175. Ka rayar da ni don in yabe ka,Ka sa koyarwarka su taimake ni!

176. Ina kai da kawowa kamar ɓatacciyar tunkiya,Ka zo ka neme ni, ni bawanka,Saboda ban ƙi kulawa da dokokinka ba.

Karanta cikakken babi Zab 119