Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:164-174 Littafi Mai Tsarki (HAU)

164. A kowace rana nakan gode maka sau bakwai,Saboda shari'unka masu adalci ne.

165. Waɗanda suke ƙaunar dokarka sun sami cikakken zaman lafiya,Ba wani abin da zai sa su fāɗi.

166. Ina jiranka ka cece ni, ya Ubangiji,Ina aikata abin da ka umarta.

167. Ina biyayya da ka'idodinka,Ina ƙaunarsu da zuciya ɗaya.

168. Ina biyayya da umarnanka da koyarwarka,Kana kuwa ganin dukan abin da nake yi.

169. Bari kukana yă kai gare ka, ya Ubangiji!Ka ganar da ni kamar yadda ka alkawarta.

170. Bari addu'ata ta zo gare ka,Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!

171. Zan yabe ka kullayauminDomin ka koya mini ka'idodinka.

172. Zan raira waƙa a kan alkawarinka,Domin umarnanka a gaskiya ne.

173. Kullum a shirye kake domin ka taimake ni,Saboda ina bin umarnanka.

174. Ina sa zuciya ga cetonka ƙwarai, ya Ubangiji!Ina samun farin ciki ga dokarka.

Karanta cikakken babi Zab 119