Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:159-167 Littafi Mai Tsarki (HAU)

159. Ka dubi yadda nake ƙaunar koyarwarka, ya Ubangiji!Ka cece ni bisa ga madawwamiyar ƙaunarka.

160. Cibiyar dokarka gaskiya ce,Dukan ka'idodinka na adalci tabbatattu ne.

161. Ƙarfafan mutane sun auka mini ba dalili,Amma maganarka ce nake girmamawa.

162. In farin ciki ƙwarai saboda alkawaranka,Farin cikina kamar na wanda ya sami dukiya mai yawa ne.

163. Ina ƙin ƙarairayi, ba na jin daɗinsu,Amma ina ƙaunar dokarka.

164. A kowace rana nakan gode maka sau bakwai,Saboda shari'unka masu adalci ne.

165. Waɗanda suke ƙaunar dokarka sun sami cikakken zaman lafiya,Ba wani abin da zai sa su fāɗi.

166. Ina jiranka ka cece ni, ya Ubangiji,Ina aikata abin da ka umarta.

167. Ina biyayya da ka'idodinka,Ina ƙaunarsu da zuciya ɗaya.

Karanta cikakken babi Zab 119