Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:15-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Nakan yi nazarin umarnanka,Nakan kuma yi bimbinin koyarwarka.

16. Ina murna da dokokinka,Ba zan manta da umarnanka ba.

17. Ka yi mini alheri, ni bawanka,Domin in rayu in yi biyayya da koyarwarka.

18. Ka buɗe idonaDomin in ga gaskiyar shari'arka mai banmamaki.

19. Zamana a nan duniya na ɗan lokaci kaɗan ne.Kada ka ɓoye mini umarnanka!

20. Zuciyata ta ƙosa saboda marmari,A kowane lokaci ina so in san hukuntanka.

21. Kakan tsauta wa masu girmankai,La'anannu ne waɗanda suka ƙi bin umarnanka.

22. Ka kuɓutar da ni daga cin mutuncinsu da raininsu,Domin na kiyaye dokokinka.

23. Ko da sarakuna za su taruSu shirya mini maƙarƙashiya,Duka da haka, ni bawanka,Zan yi nazarin ka'idodinka.

24. Umarnanka suna faranta mini rai,Su ne mashawartana.

25. Ina kwance cikin ƙura, an yi nasara da ni,Ka wartsakar da ni kamar yadda ka alkawarta!

26. Na hurta dukan abin da na aikata, ka kuwa amsa mini,Ka koya mini ka'idodinka!

27. Ka koya mini yadda zan yi biyayya da dokokinka,In kuma yi nazarin koyarwarka mai banmamaki.

Karanta cikakken babi Zab 119